54 Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, "An haɗiye mutuwa cikin nasara."15.54 Ish 25.8
55 "Ya ke mutuwa, ina nasararki?
Ya ke mutuwa, ina dafinki?"15.55 Hos 13.14
56 Zunubi ne yake ba wa mutuwa dafi, Doka kuma take ba wa zunubi iko. 57 Amma godiya ga Allah! Shi ne ya ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.