6 A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri. 7 Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi. 8 Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi, 9 gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.