2 Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen sha’awace-sha’awacen jiki, sai dai nufin Allah. 3 Gama kun ɓata lokaci sosai a dā kuna yin abubuwan da masu bauta gumaka suka zaɓa su yi, kuna rayuwa cikin lalata, sha’awace-sha’awace, buguwa, shashanci, shaye-shaye da kuma bautar gumaka masu banƙyama. 4 Sun yi mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, da ba kwa kutsa kai tare da su cikin irin rayuwar banzan nan, har suna zaginku. 5 Amma dole su ba da lissafi gare shi wanda yake a shirye yă shari’anta masu rai da matattu. 6 Dalilin ke nan da ya sa aka yi wa’azin bishara har ga waɗanda yanzu suke mutattu, don ko da yake an hukunta su a matsayin mutane a batun jiki, amma su rayu ga Allah a batun ruhu.
7 Ƙarshen abubuwa duka ya yi kusa. Saboda haka ku kasance masu tunani mai kyau da masu kamunkai don ku iya yin addu’a.