4 Wani jarumin da ake kira Goliyat wanda ya fito daga Gat, ya fita daga sansanin Filistiyawa. Tsawonsa ya fi ƙafa tara.
33 Shawulu ya ce, "Ba za ka iya yin faɗa da wannan Bafilistin ba, ya daɗe yana yaƙi, ya yi yaƙi tun yana saurayi. Ga shi kuwa kai ɗan yaro ne kawai."
37 Ubangiji wanda ya cece ni daga kumbar zaki da kuma kumbar beyar, zai cece ni daga hannun wannan Bafilistin."
Shawulu ya ce wa Dawuda, "Je ka, Ubangiji yă kasance tare da kai."
40 Sai ya ɗauki sandansa, ya zaɓi duwatsu guda biyar masu sulɓi daga cikin rafi, ya sa su a ’yar jakarsa ta makiyaya; ya kuma ɗauki majajjawarsa, ya tafi, yă fuskanci Bafilistin.
45 Dawuda ya ce wa Bafilistin, "Kana zuwa ka yaƙe ni da māshi da takobi da kere, amma ni ina zuwa in yaƙe ka a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki, Allah na rundunar Isra’ila, wanda ka rena.
49 Ya sa hannu a jakarsa ya ɗauki dutse, ya sa cikin majajjawa ya wurga, dutsen kuwa ya bugi Bafilistin a goshi, dutsen ya shiga cikin goshinsa, sai Bafilistin ya fāɗi rubda ciki.