Shawulu ya fara kishin Dawuda
1 Bayan da Dawuda ya gama magana da Shawulu, sai Yonatan ɗan Shawulu ya ji zuciyarsa tana son Dawuda sosai. Yonatan kuwa yana ƙaunar Dawuda kamar ransa. 2 Tun daga wannan rana Shawulu ya zaunar da Dawuda tare da shi, bai bar shi ya koma gidan mahaifinsa ba. 3 Yonatan kuma ya yi yarjejjeniya da Dawuda saboda yana ƙaunarsa kamar ransa.