Pular para o conteúdo
Publicidade

1 Samuel 20

41 Da yaron ya tafi, sai Dawuda ya tashi daga inda ya ɓuya kusa da tarin duwatsu, ya rusuna har sau uku. Sa’an nan suka sumbaci juna, suka yi kuka, Dawuda kuwa ya yi kuka sosai.

42 Yonatan ya ce wa Dawuda, "Sauka lafiya, mun riga mun yi rantsuwar abokantaka da juna a cikin sunan Ubangiji cewa, Ubangiji ne shaida tsakanina da kai, tsakanin zuriyarka da zuriyata har abada.’ " Sai Dawuda ya tafi, Yonatan kuwa ya koma gari.

Veja também