16 Yonatan ɗan Shawulu kuwa ya tafi wurin Dawuda a Horesh, ya ƙarfafa shi yă dogara ga Allah. 17 Ya ce, "Kada ka ji tsoro, mahaifina Shawulu ba zai taɓa sa hannu a kanka ba. Za ka zama sarki a Isra’ila, ni kuma in zama na biyu gare ka. Kai, ko mahaifina Shawulu ma ya san da haka." 18 Su biyunsu kuwa suka ɗaura yarjejjeniya a gaban Ubangiji. Sai Yonatan ya koma gida amma Dawuda ya zauna Horesh.
Publicidade