32 Dawuda ya ce wa Abigiyel, "Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya aiko ki don ki same ni yau. 33 Bari Allah yă albarkace ki saboda hikima yanke hukuncinki da kuma hana ni zubar da jini da ɗauka wa kaina fansa da hannuna a wannan rana.