An komar da akwatin alkawari a Isra’ila
1 Lokacin da akwatin alkawarin Ubangiji ya kai wata bakwai a ƙasar Filistiyawa. 2 Filistiyawa suka kira firistoci da bokaye suka ce, "Me za mu yi da akwatin alkawarin Ubangiji? Ku gaya mana yadda za mu komar da shi inda ya fito."
3 Suka ce, in za ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila kada ku komar da shi hannu wofi; amma ku tabbata kun aika da hadaya don laifi zuwa wurinsa. Sa’an nan za ku warke ku kuma san dalilin da ya sa bai cire hannunsa a kanku ba.