Godiya saboda bangaskiyar Tessalonikawa
2 Kullum muna gode wa Allah dominku duka, muna ambatonku cikin addu’o’inmu. 3 Muna tunawa da aikinku ba fasawa a gaban Allah da Ubanmu ta wurin bangaskiya, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begenku marar gushewa ga Ubangijinmu Yesu Kiristi.