16 Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. 17 Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada.
Publicidade
Publicidade