1 To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku, 2 gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare. 3 Yayinda mutane suke cewa, "Akwai salama da zaman lafiya," hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.
Publicidade