Pular para o conteúdo
Publicidade

1 Tessalonicenses 5

1 To, yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku, 2 gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za zo kamar ɓarawo da dare. 3 Yayinda mutane suke cewa, "Akwai salama da zaman lafiya," hallaka za auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.

4 Amma ku, yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za zo muku ba zato kamar ɓarawo. 5 Dukanku ya’yan haske ne da kuma ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne.

Veja também

1 Tessalonicenses
Ver todos os capítulos de 1 Tessalonicenses