4 Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo. 5 Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne. 6 Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai. 7 Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa. 8 Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano. 9 Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
Publicidade