17 Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo! 18 Duk wannan kuwa daga Allah ne, wanda ya sulhunta mu da kansa ta wurin Kiristi, ya kuma ba mu hidimar sulhu, 19 wato, Allah ya sulhunta duniya zuwa kansa ta wurin Kiristi, ba ya lissafta zunuban mutane a kansu. Ya kuma danƙa mana saƙon sulhu. 20 Saboda haka, mu jakadu ne na Kiristi, sai ka ce Allah kansa yake magana ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Kiristi. Ku sulhuntu da Allah. 21 Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa.
Publicidade