Pular para o conteúdo
Publicidade

2 Korintiyawa 6:14-17

Kada ku haɗa kai da marasa bi

14 Kada ku haɗa kai da marasa bi. Gama me ya haɗa adalci da mugunta? Ko kuwa me ya haɗa haske da duhu? 15 Wace daidaituwa ce tsakanin Kiristi da Iblis? Me ya haɗa mai bi da marar bi? 16 Wane alkawari ne tsakanin haikalin Allah da na gumaka? Gama mu haikalin Allah mai rai ne. Kamar yadda Allah ya ce,

"Zan zauna tare da su,

in yi tafiya a cikinsu,

zan zama Allahnsu,

su kuma za su zama mutanena."6.16 Fir 26.12; Irm 32.38; Ezk 37.27

17 Saboda haka,

"Sai ku fito daga cikinsu,

ku keɓe kanku,

in ji Ubangiji.

Kada ku taɓa wani abu marar tsabta,

zan kuma karɓe ku."6.17 Ish 52.11; Ezk 20.34,41

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.