Ruwan warkarwa
19 Mutane garin suka ce wa Elisha, "Ranka yă daɗe, duba, garin yana da kyan gani, amma ruwan ba shi da kyau, ƙasar kuma ba ta ba da amfani."
20 Sai ya ce, "Ku kawo mini sabuwar ƙwarya, ku kuma sa gishiri a ciki." Sai suka kawo masa.
21 Sai ya tafi maɓulɓular ruwan yana watsa gishirin a ciki, yana cewa, "Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Na warkar da ruwan nan. Ba zai ƙara jawo mutuwa, ko yă hana ƙasar ba da amfani ba.’ " 22 Ruwan ya tsabtacce har yă zuwa yau, bisa ga faɗin Elisha.