An maido da ɗan mutuniyar Shunem da rai
8 Wata rana Elisha ya tafi Shunem. Akwai wata mai arziki a can wadda ta gayyace shi cin abinci. Sai ya zama duk lokacin da yake wucewa, yakan tsaya a can don cin abinci. 9 Ta ce wa mijinta, "Na san cewa wannan mutum da kullum yake zuwa nan mai tsarki ne na Allah. 10 Bari mu yi ɗan ɗaki a rufin gida mu kuma sa masa gado da tebur da kujera da kuma fitila. Saboda a duk lokacin da ya zo wurinmu, sai yă sauka a can."
11 Wata rana da Elisha ya zo, sai ya haura ɗakinsa ya kwanta. 12 Ya ce wa bawansa Gehazi, "Kira mutuniyar Shunam nan." Sai ya kira ta, ta zo ta tsaya a gabansa. 13 Elisha ya ce masa, "Ka ce mata, ‘Kin yi duk wannan ɗawainiya saboda mu. Yanzu, me kike so a yi miki? Kina so mu yi magana a madadinki wa sarki ko babban hafsan mayaƙa?’ "
Sai ta ce, "A’a, ina da dukan abin da nake bukata a cikin jama’ata."
14 Sai Elisha ya tambayi Gehazi ya ce, "Me za mu yi mata?"
Sai ya amsa ya ce, "Ba ta da ɗa, ga shi kuma mijinta ya tsufa."
15 Sai Elisha ya ce, "Ka kira ta." Sai ya kira ta, ta zo ta tsaya a bakin ƙofa. 16 Elisha ya ce mata, "War haka baɗi, za ki riƙe ɗa na kanki."
Sai ta ce masa, "A’a, ranka yă daɗe, mutumin Allah, kada ka ruɗi baiwarka!"
17 Amma matan ta yi ciki, a shekara ta biye kuwa a daidai lokacin, sai ta haifi ɗa kamar yadda Elisha ya faɗa mata.
18 Yaron ya yi girma, wata rana sai ya tafi wurin mahaifinsa, wanda yake tare da masu girbi. 19 Ba zato sai ya ce wa mahaifinsa, "Wayyo! Kaina yana mini ciwo! Kaina yana mini ciwo!"
Sai mahaifinsa ya ce wa bawansa, "Kai shi wurin mahaifiyarsa." 20 Bayan bawan ya ɗaga shi ya kai wurin mahaifiyarsa, sai yaron ya zauna a cinyarta har tsakar rana, sa’an nan ya mutu. 21 Sai ta haura ta shimfiɗa shi a gadon mutumin Allah, ta rufe ƙofar, ta fita.
22 Ta kira mijinta ta ce, "Ina roƙonka ka aika mini da ɗaya daga cikin bayi da kuma jaka, don in yi sauri in je wurin mutumin Allah in dawo."
23 Sai ya ce, "Me zai kai ki wurinsa, ai, yau ba Sabon Wata ba ne ko ranar Asabbaci?"
Sai ta ce, "Ba kome."
24 Sai ta sa wa jakar sirdi ta ce wa bawanta, "Yi ta kora mini jakar, kada ka sassauta, sai na faɗa maka." 25 Ta haka ta kama hanya ta tafi wurin mutumin Allah a Dutsen Karmel.
Da ya hange ta daga nesa, sai mutumin Allah ya ce wa bawansa Gehazi, "Duba! Ga mutuniyar Shunam nan can! 26 Ka yi gudu ka tarye ta ka tambaye ta, ‘Lafiyarki? Mijinki yana nan lafiya? Yaronki yana nan lafiya?’ "
Ta amsa ta ce, "Kome lafiya yake."
27 Da ta isa wurin mutumin Allah a dutsen, sai ta kama ƙafafunsa. Sai Gehazi ya zo don yă ture ta, amma mutumin Allah ya ce, "Ka bar ta! Tana cikin baƙin ciki ƙwarai, amma Ubangiji ya ɓoye mini, bai kuma faɗa mini me ya sa ba."
28 Sai ta tambaya shi ta ce, "Na roƙe ka ɗa ne, ranka yă daɗe? Ba na ce maka, ‘Kada ka sa in fara bege ba’?"
29 Elisha ya ce wa Gehazi, "Ka yi ɗamara, ka ɗauki sandana ka ruga a guje. Idan ka sadu da wani, kada ka gaishe shi, idan kuma wani ya gaishe ka, kada ka amsa. Ka shimfiɗa sandana a fuskar yaron."
30 Amma mahaifiyar yaron ta ce, "Muddin Ubangiji yana raye, kai kuma kana a raye, ba zan bar ka ba." Saboda haka ya tashi ya bi ta.
31 Gehazi ya yi gaba, ya shimfiɗa sandan a fuskar yaron, amma babu motsi, babu alamar rai. Saboda haka Gehazi ya koma ya taryi Elisha, ya faɗa masa, "Yaron bai tashi ba."
32 Da Elisha ya isa gidan, sai ga gawar yaron kwance a kan gadonsa. 33 Sai ya shiga, ya rufe ƙofa, daga shi sai yaron, ya kuma yi addu’a ga Ubangiji. 34 Sa’an nan ya hau gadon yă kwanta a bisa yaron, ya miƙe a kansa, baki da baki, ido da ido, hannu da hannu. Yayinda ya miƙe kansa a kan yaron, sai jikin yaron ya ɗau ɗumi. 35 Elisha ya tashi, ya yi ta kai komo a cikin ɗakin. Sa’an nan ya sāke koma kan gadon yă miƙe a kan yaron, sai yaron ya yi atishawa sau bakwai, ya kuma buɗe idanunsa.
36 Elisha ya kira Gehazi ya ce, "Kirawo mutuniyar Shunam." Ya kuwa kira ta. Sa’ad da ta zo, sai Elisha ya ce mata, "Ɗauki ɗanki." 37 Sai ta shiga, ta fāɗi a ƙafafunsa ta rusuna har ƙasa. Sa’an nan ta ɗauki ɗanta ta fita.