Pular para o conteúdo
Publicidade

2 Reis 6

Kan gatari ya yi yawo a kan ruwa

1 Sai ƙungiyar annabawa suka ce wa Elisha, "Duba, wurin da muke taruwa ya kāsa mana. 2 Bari mu je Urdun, inda kowannenmu zai saro itace; mu gina inda za mu zauna."

Sai ya ce musu, "Ku je."

3 Sai ɗayansu ya ce, "Ba za ka zo tare da bayinka ba?"

Sai Elisha ya ce "Zan zo." 4 Ya kuma tafi tare da su.

Suka tafi Urdun suka fara saran itatuwa. 5 Yayinda ɗayansu yake cikin saran itace, sai kan gatarin ya fāɗi a ruwa, sai ya ce, "Kash, ranka daɗe, kayan aro ne fa!"

6 Sai mutumin Allah ya ce, "Daidai ina ya fāɗa?" Da ya nuna masa wurin, sai Elisha ya yanka ɗan sanda ya jefa a wurin, ya sa kan gatarin ya taso sama. 7 Sai ya ce masa, "Ka ɗauko." Sai mutumin ya miƙa hannu ya ɗauka.

Veja também