Publicidade

2 Timóteo 3

Rashin sanin Allah a kwanakin ƙarshe

1 Amma fa ka san wannan, za a yi lokutan shan wahala a kwanakin ƙarshe. 2 Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki, 3 marasa ƙauna, marasa gafartawa, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kamunkai, masu ƙeta, marasa ƙaunar nagarta, 4 masu cin amana, marasa hankali, waɗanda sun cika da ɗaga kai, masu son jin daɗi a maimakon ƙaunar Allah 5 suna riƙe da siffofin ibada, amma suna mūsun ikonta. Kada wani abu haɗa ka da su.

Veja também

2 Timóteo
Ver todos os capítulos de 2 Timóteo
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-