Mutumin tawayen nan
1 Game da dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi da game da tattara mu gare shi, muna roƙonku, ’yan’uwa, 2 kada ku yi saurin jijjiguwa ko kuwa hankalinku yă tashi ta wurin wani annabci, rahoto ko wasiƙar da an ce daga wurinmu ne, cewa ranar Ubangiji ta riga ta zo. 3 Kada ku bar wani yă ruɗe ku ko ta yaya, gama wannan rana ba za tă zo ba sai an yi tawayen nan an kuma bayyana mutumin tawayen nan, mutumin da aka ƙaddara ga hallaka. 4 Zai yi gāba yă kuma ɗaukaka kansa a bisa kome da ya shafe sunan Allah, ko kuma ake yi wa sujada, domin yă kafa kansa a haikalin Allah, yana shelar kansa a kan shi Allah ne.