Roƙo don addu’a
1 A ƙarshe, ’yan’uwa, ku yi mana addu’a domin saƙon Ubangiji yă yi saurin bazuwa a kuma girmama shi, kamar yadda yake a wurinku. 2 Ku kuma yi addu’a yadda za a cece mu daga mugayen mutane masu mugunta, gama ba kowa ba ne yake da bangaskiya.