10 Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, "In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci."
11 Mun ji cewa waɗansunku suna zaman banza. Ba sa aikin kome; sai shisshigi kurum. 12 Irin waɗannan mutane muna ba da umarni muna kuma gargaɗe su cikin Ubangiji Yesu Kiristi su natsu su kuma nemi abincin da suke ci. 13 Game da ku kuma ’yan’uwa, kada ku gaji da yin abin da yake daidai.