8 Ni, Yohanna, na ji, na kuma ga abubuwan nan. Kuma sa’ad da na ji, na kuma gan su, sai na fāɗi a ƙasa a gaban mala’ikan da yake nuna mini su, don in yi sujada. 9 Amma ya ce mini, "Kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da ’yan’uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye kalmomin wannan littafi. Allah za ka yi wa sujada!"