15 Na san ayyukanka, ba ka da sanyi ba ka kuma da zafi. Na so da kai ɗaya ne daga ciki, ko sanyi, ko zafi! 16 Amma domin kana tsaka-tsaka ba zafi ba, ba kuma sanyi ba, ina dab da tofar da kai daga bakina. 17 Ka ce, ‘Ina da arziki; na sami dukiya ba na kuma bukatar kome.’ Amma ba ka gane ba cewa kai matsiyaci ne, abin tausayi, matalauci, makaho kana kuma tsirara.
20 Ga ni! Ina tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa. Duk wanda ya ji muryata ya kuma buɗe ƙofar, zan shiga in kuma ci tare da shi, shi kuma tare da ni.