12 Ina kallo yayinda ya buɗe hatimi na shida. Sai aka yi babban girgizar ƙasa. Rana ta zama baƙa kamar gwado na gashin akuya, wata kuma gaba ɗaya ya zama ja wur kamar jini, 13 taurarin sararin sama suka fāffāɗi a ƙasa, kamar yadda ɗanyun ’ya’yan ɓaure suke fāɗuwa daga itacen ɓaure sa’ad da iska mai ƙarfi ta jijjiga shi.