36 Yayinda suke cikin tafiya a kan hanya, sai suka iso wani wurin ruwa bābān nan ya ce, "Duba, ga ruwa. Me zai hana a yi mini baftisma?"8.36 Waɗansu rubuce-rubucen hannu da da ba su daɗe ba suna da baftisma? 37 Filibus ya ce, "In ka gaskata da dukan zuciyarka, za ka iya." Bābān ya ce, "Na gaskata cewa Yesu Kiristi shi ne Ɗan Allah." 38 Ya kuwa ba da umarni a tsai da keken yaƙin. Sa’an nan da Filibus da bābān suka gangara zuwa cikin ruwan Filibus kuwa ya yi masa baftisma.
Publicidade