Pular para o conteúdo
Publicidade

Ayyukan Manzanni 8

5 Filibus ya gangara zuwa wani birni a Samariya ya kuma yi shelar Kiristi a can. 6 Sa’ad da taron mutane suka ji Filibus suka kuma ga abubuwan banmamakin da ya yi, sai duk suka mai da hankali sosai ga abin da ya faɗa. 7 Mugayen ruhohi suka fiffito suna kururuwa daga cikin mutane da yawa, shanyayyu da guragu masu yawa suka sami warkarwa. 8 Saboda haka aka yi farin ciki ƙwarai a birnin.

Veja também