5 Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne. 6 Gama fushin Allah zai sauko a kan masu aikata waɗannan.3.6 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da zuwa a kan waɗanda suke rashin biyayya 7 Dā kun yi waɗannan abubuwa, sa’ad da rayuwar tana cikin duniya mai wannan hali. 8 Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku. 9 Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa
Publicidade