5 "Sai sarki Kudu zai yi ƙarfi ƙwarai, amma ɗaya daga cikin komandodinsa zai yi ƙarfi fiye da shi, zai kuma yi mulki masarautarsa da iko mai girma. 6 Bayan ’yan shekaru, za su haɗa kai. Diyar sarkin Kudu za tă je wurin sarkin Arewa ta sada zumunci, amma ba za tă riƙe iko ba, shi kuwa da ikonsa11.6 Ko kuwa zuriyarsa ba za su daɗe ba. A waɗannan kwanaki za a bashe ta, da ita da masu rakiyarta da kuma mahaifinta11.6 Ko kuwa yaro (dubi Bulget da Siriyak) da kuma wanda ya goyi bayanta.