Publicidade

Daniel 12

Ƙarshe zamani

1 "A wannan lokaci Mika’ilu, babban mai mulki wanda yake kāre mutanenka, zai tashi. Za a yi lokacin matsananciyar wahala wanda ba a taɓa yi tun farkon ƙasashe har zuwa yanzu. Amma a lokacin da mutanenka, kowane mutum wanda aka sami sunansa a rubuce a cikin littafin, za a cece shi. 2 Ɗumbun mutanen da suka yi barci cikin turɓayar duniya za su farka, waɗansu zuwa ga rai madawwami, waɗansu zuwa ga madawwamiyar kunya da kuma madawwamin ƙasƙanci. 3 Waɗanda suke da hikima12.3 Ko kuwa waɗanda suke ba da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-