13 "A wahayina na dare, na ga a gabana wani kamar ɗan mutum7.13 Kalmomin Arameyik nan bar enash suna nufin mutum. Kalmomin nan ɗan mutum an yi amfani da su a nan saboda a amfanin da aka yi da su a Sabon Alkawari a matsayi wakilin suna na Yesu, mai yiwuwa saboda dangane a kan wannan ayar. yana saukowa tare da gizagizan sama. Ya kusaci Wannan wanda yake Tun fil azal aka kuma kai shi gabansa. 14 Aka ba shi mulki, daraja da kuma mafificin iko; dukan mutane, da al’ummai, da mutane daga kowane harshe suka yi masa sujada. Mulkinsa kuwa dawwammamen mulki ne da ba zai ƙare ba, sarautarsa kuma ba ta taɓa lalacewa.