9 "Ina cikin dubawa,
"sai aka ajiye kursiyoyi,
sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa.
Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara;
gashin kansa sun yi fari kamar ulu.
Kursiyinsa kuma harshen wuta,
dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne.