18 Saboda haka, sai ku riƙe waɗannan kalmomina gam a zukatanku da ranku; ku ɗaura su kamar alama a hannuwanku, da goshinku. 19 Ku koyar da su ga ’ya’yanku, ku yi ta haddace su, sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi. 20 Ku rubuta su a kan madogaran ƙofofin gidajenku, da a kan ƙofofinku, 21 saboda kwanakinku da kwanakin ’ya’yanku su yi tsawo a ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninku, muddin sama tana bisa duniya.
Publicidade