Dokoki game da hana lalata
13 In mutum ya auri mace, bayan ya kwana da ita, sa’an nan ya ƙi ta 14 ya kuma zarge ta, ya ba ta mummunan suna, yana cewa, "Na auri wannan mata, amma sa’ad da na kusace ta, ban sami tabbaci cewa ita budurwa ba ce," 15 sai mahaifin yarinyar da mahaifiyarta su kawo shaida cewa ita budurwa ce wa dattawan gari a ƙofar garin. 16 Mahaifin yarinyar zai ce wa dattawa, "Na ba da ’yata aure ga wannan mutum, amma ya ƙi ta. 17 Yanzu ya zage ta cewa, ‘Ban sami ’yarku budurwa ba.’ Amma ga shaidar budurcin ’yata." Sa’an nan iyayenta za su shimfiɗa zanen a gaban dattawan garin,