Pular para o conteúdo
Publicidade

Afisawa 2

An sulhunta Yahudawa da al’ummai su zama ɗaya ta wurin Kiristi

11 Saboda haka, ku tuna ku Al’ummai ne bisa ga haihuwa, waɗanda kuma ake kira masu "kaciya" sukan kira ku "marasa kaciya" (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu). 12 Ku kuma tuna a lokacin ba ku san Kiristi ba. A ware kuke daga mutanen Isra’ila, ba ku kuma da dangantaka da alkawaran da Allah ya yi da su. Kun yi zama a duniyan nan babu bege kuma babu Allah. 13 Amma yanzu a cikin Kiristi Yesu, ku da kuke can da nesa an kawo ku kusa ta wurin jinin Kiristi.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também