16 Ina addu’a cewa daga yalwar ɗaukakarsa zai ƙarfafa ku da iko daga ciki ta wurin Ruhunsa. 17 Ina addu’a domin Kiristi yă zauna a cikin zukatanku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu’a saboda ku da kuka kahu sosai cikin ƙauna, 18 don ku sami iko, tare da dukan tsarkaka, ku fahimci fāɗi, tsawo, da kuma zurfin ƙaunar Kiristi take. 19 Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan cikar Allah.