25 Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta. 26 Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa. 27 Kiristi ya yi haka don yă miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma mai tsarki, marar aibi, marar tabo, da kuma marar lahani. 28 Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne. 29 Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yă ciyar da shi, yă kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya, 30 gama mu gaɓoɓin jikinsa ne.