Pular para o conteúdo
Publicidade

Afisawa 5

28 Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne. 29 Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai ciyar da shi, kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya, 30 gama mu gaɓoɓin jikinsa ne. 31 "Saboda haka mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, manne wa matarsa, su biyun su zama jiki ɗaya."5.31 Far 2.24 32 Wannan babban asiri ne, amma na ɗauke shi a matsayin kwatanci ne na Kiristi da ikkilisiya. 33 Duk da haka, dole kowannenku ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar yi biyayya ga mijinta.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também