’Ya’ya da iyaye
1 Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. 2 Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, "Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, 3 don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya."6.3 M Sh 5.16