Pular para o conteúdo
Publicidade

Efésios 6

Ya’ya da iyaye

1 Ku ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. 2 Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, "Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, 3 don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya."6.3 M Sh 5.16

4 Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.

Veja também