Pular para o conteúdo
Publicidade

Efésios 6

13 Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge. 14 Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya zama ɗamararku, adalci zama sulkenku, 15 shirin kai bisharar salama zama kamar takalmi a ƙafafunku. 16 Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. 17 Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.

18 A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a.

Veja também