Pular para o conteúdo
Publicidade

Fitowa 12

24 "Ku kiyaye waɗannan dokokin a matsayin dawwammamiyar farilla, da ku da ya’yanku har abada. 25 Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji zai ba ku yadda ya alkawarta, ku kiyaye wannan biki. 26 Sa’ad da kuma ya’yanku suka tambaye ku, Mece ce manufar wannan biki?27 Sai ku faɗa musu, Hadaya ce ta Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra’ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba.’ " Sai mutane suka rusuna, suka yi sujada.

Veja também