Pular para o conteúdo
Publicidade

Êxodo 16

11 Ubangiji ya ce wa Musa, 12 "Na ji gunagunin Isra’ilawa. Ka faɗa musu, A tsakanin fāɗuwar rana da almuru, za ku ci nama, da safe kuma za ku ƙoshi da burodi. Sa’an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku.’ "

13 Da yamman wannan rana, sai makware suka rufe dukan sansani, da safe kuma sai ga raɓa ta kewaye sansani. 14 Lokacin da raɓar ta watse, sai ga wani abu kamar tsaki, falle-falle kuma da laushi, fari, kamar hazo, a ƙasa. 15 Sa’ad da Isra’ilawa suka ga wannan, sai suka ce wa junansu, "Mene ne wannan?" Gama ba su san ko mene ne ba.

Musa ya ce musu, "Wannan shi ne burodin da Ubangiji ya ba ku ku ci.

Veja também