Pular para o conteúdo
Publicidade

Fitowa 2

Haihuwar Musa

1 Ana nan, sai wani Balawe ya auri wata Balawiya, 2 ta kuwa yi ciki, ta haifi ɗa. Sa’ad da ta ga jaririn kyakkyawa ne, sai ta ɓoye shi har watanni uku. 3 Amma da ba iya ɓoye shi kuma ba, sai ta yi kwandon kyauro ta shafa masa kwalta. Bayan haka sai ta sa jaririn a cikin kwandon, ta je ta ajiye kwandon tare da jaririn a cikin kyauro, a bakin kogin. 4 Yar’uwarsa ta tsaya da ɗan rata tana lura da abin da zai faru da shi.

5 Sai yar Fir’auna ta gangara zuwa kogi domin yi wanka, bayinta kuwa suna tafiya a bakin kogi. Sai ta ga kwandon a ciyawa, ta aiki ɗaya daga cikin masu hidimarta ɗauko mata. 6 Da ta buɗe kwandon, sai ta ga yaro yana kuka, ta kuwa ji tausayinsa. Ta ce, "Wannan ɗaya daga cikin jariran Ibraniyawa ne."

7 Sai yar’uwarsa ta tambayi yar Fir’auna, ta ce, "In tafi in samo ɗaya daga cikin matan Ibraniyawa yi miki renon yaron?"

8 Sai ta amsa ta ce, "I, tafi." Sai yarinyar ta tafi ta kawo mahaifiyar yaron. 9 Diyar Fir’auna ta ce mata, "Ɗauki jaririn, ki yi mini renonsa, zan kuwa biya ki." Saboda haka ta ɗauki yaron, ta yi renonsa. 10 Sa’ad da ya yi girma, sai ta kawo shi wajen yar Fir’auna, ya kuwa zama ɗanta, ta kuma ba shi suna Musa, tana cewa, "Na tsamo shi daga ruwa."

Veja também