Akwatin alkawari
10 "Ka sa a yi akwatin alkawarin da itacen ƙirya, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kamu ɗaya da rabi, tsayinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 11 Ka dalaye shi da zinariya zalla ciki da waje, za ka yi wa gefe-gefensa ado da gurun zinariya. 12 Ka kewaye akwatin da zoban zinariya huɗu ka kuma haɗa su da ƙafafunsa huɗu, zobai biyu a kowane gefe. 13 Sa’an nan ka yi sanduna da itacen ƙirya, ka dalaye su da zinariya. 14 Ka sa sandunan a cikin zoban, a gefen akwatin domin ɗaukansa. 15 Sanduna za su kasance a cikin waɗannan zoban akwatin alkawarin; ba za a cire su ba. 16 Sa’an nan ka sa Shaidar da zan ba ka, a cikin akwatin.
17 "Ka yi murfin kafara da zinariya zalla, tsawonsa kamu biyu da rabi, fāɗinsa kuma kamu ɗaya da rabi. 18 Ka kuma yi kerubobi biyu da zinariyar da aka ƙera, ka sa a gefen nan biyu na murfin. 19 Ka yi kerubobi biyu, ɗaya a wannan gefe, ɗaya kuma a ɗayan gefen; za ka manne su a kan murfin, su zama abu ɗaya. 20 Kerubobin su kasance da fikafikansu a buɗe, domin su inuwantar da murfin, za su fuskanci juna, suna duba murfin. 21 Ka sa murfin a bisa akwatin ka kuma sa allunan dokokin alkawarin da zan ba ka a ciki.