Pular para o conteúdo
Publicidade

Fitowa 27:1-8

Bagaden hadaya ta ƙonawa

1 "Ka gina bagade da itacen ƙirya, mai tsawo kamu uku, zai zama murabba’i, mai tsawo kamu biyar, fāɗi kuma kamu biyar. 2 Ka yi masa ƙaho a kowace kusurwan nan huɗu, domin bagade da ƙahoni duk su zama ɗaya, ka dalaye bagade da tagulla. 3 Ka yi duk kayan aikinsa da tagulla, tukwanensa na ɗiban toka, da manyan cokula, da kwanonin yayyafawa, da cokula masu yatsotsi don nama da kuma farantai domin wuta. 4 Ka yi raga na tagulla dominsa, ka kuma yi zoben tagulla a kowace kusurwan nan huɗu na bagaden. 5 Ka sa ragar a ƙarƙashin bagade domin tă kai tsakiyar bagade. 6 Ka yi wa bagaden sanduna da itacen ƙirya, ka dalaye su da tagulla. 7 Za a zura sandunan a cikin zoban saboda su kasance a gefe biyu na bagade a lokacin da ake ɗaukarsa. 8 Ka yi bagaden da katakai, sa’an nan ka robe cikinsa. Ka yi shi bisa ga fasalin da aka nuna maka a bisa dutsen.

Filin tabanakul

(Fitowa 38.9-20)

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.