Pular para o conteúdo
Publicidade

Filibbiyawa 2

Haskaka kamar taurari

12 Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki, 13 gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.

14 Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba, 15 don ku zama marasa abin zargi, sahihai ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya 16 kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também

Filipenses
Ver todos os capítulos de Filipenses