11 Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. 12 Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. 13 Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.