13 Ku ’yan’uwana, an kira ku ga zama ’yantattu. Amma kada ku yi amfani da ’yancinku don aikata ayyukan mutuntaka5.13 Ko kuwa na jiki; haka ma a ayoyi 16, 17, 19 da 24 a maimakon haka, ku yi hidimar juna da ƙauna. 14 Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya ne cewa, "Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka."5.14 Fir 19.18